John 10

1“Hakika, Hakika, ina ce maku, wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi. 2Wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin.

3Mai gadin kofar zai bude masa. Tumakin suna jin muryarsa, ya na kuma kiran tumakinsa da sunayensu, ya kuma kai su waje. 4Bayanda ya kawo su duka a waje, yana tafiya a gabansu, sai tumakin su bi shi, domin sun san muryarsa.

5Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba.” 6Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba.

7Sai Yesu ya ce masu kuma, “Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki. 8Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba.

9Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo. 10Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace.

11Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa. 12Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su. 13Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba.

14Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni. 15Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin. 16Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya.

17Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma. 18Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana.”

19Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin. 20Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?” 21Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?”

22Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo. 23A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu. 24Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, “Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla.”

25Yesu ya ce masu, “Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina. 26Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.

27Tumakina suna jin murya ta; Na san su, suna kuma bi na. 28Ina ba su rai na har abada; ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu na.

29Ubana, wanda ya bani su, ya fi kowa girma, kuma ba mai iya kwace su daga hannun Uban. 30Ni da Uban daya ne.” 31Sai Yahudawa suka dauki duwatsu kuma domin su jajjefe shi.

32Yesu ya amsa masu, “Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban. Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?” 33Sai Yahudawa suka amsa masa, “ba don wani aiki mai kyau muke son mu jefe ka ba, amma don sabo, domin kai, mutum ne, amma kana mayar da kanka Allah.”

34Yesu ya amsa masu, “Ba a rubuce yake a shari’arku ba, ‘Na ce, “ku alloli ne“’?” 35In ya kira su alloli, su wadanda maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba), 36kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, ‘Kana sabo’, domin Na ce, ‘Ni dan Allah ne’?

37In ba na aikin Ubana, kada ku gaskata ni. 38Amma, idan ina yin su, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan saboda ku sani, ku kuma gane cewa Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban.” 39Suka sake kokarin kama shi, amma ya yi tafiyarsa, ya fita daga hannunsu.

40Ya yi tafiyarsa kuma har gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada, ya kuma zauna a wurin. 41Mutane masu yawa suka zo wurinsa, suka ce,”Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne.” Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.

42

Copyright information for HauULB